Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi matukar kaduwa da halin da ya tarar da babban asibitin garin Gwoza ke ciki na rashin hasken wutar lantarki da sauran wasu abubuwa.
Gwamnan ya yi dirar mikiya a asibitin ne a daren jiya Asabar a wata ziyarar aiki da ya kai karamar hukumar Gwoza na kwana daya, inda ya kwana a garin da ke kudancin Borno.
Ba wannan ne karon farko da Zulum ke kai ziyaya bazata ba, dabi’arsa ce hakan kuma ya kai irin wannan ziyara ba adadi a asibitoci da makarantu yayin da ake tsaka da aiki duk da zummar gane wa idanunsa yadda abubuwa ke tafiya.
A ziyarar da ya kai, Zulum ya zagaya lungu da sakon babban asibitin cikin daren jiya domin tantance ayyukan asibitin da kuma halin da marasa lafiya ke ciki.




A cewar jawabin da Jami’in Yada Labaransa Abdurrahman Ahmed Mundi ya fitar a safiyar yau Lahadi, Gwamna Zulum ya yi takaicin abin da ya gani a ziyarar.
“Ba abin yarda ba ne a ce cibiyar kiwon lafiya mai matukar muhimmanci kamar wannan babban asibitin Gwoza an hana shi kayayyakin more rayuwa kamar wutar lantarki. Wannan yanayin yana lalata ingancin kulawar da ake ba marasa lafiya kuma yana kawo cikas ga ƙoƙarin kwararrun likitocinmu na kiwon lafiya. Ba mu zo nan don daora zargi akan kowa ba, mun zo ne don nemo mafita. Babu wanda ya taba sanar da ni halin da ake ciki a wannan wuri,” in ji Zulum cikin fushi.
Ya kara da cewa, “Ba zan wanke kaina ko karamar hukuma ba. Mu (dukkanmu) mun kasa samar da abin da ake bukata. Sai dai ina so na tabbatar muku (marasa lafiya da sauran jama’a) cewa insha Allahu za mu gyara, za mu kyautata yanayin aiki a nan fiye da yadda yake a yanzu.”
Daga karahe a cikin daren jiya ya bada umarnin a fara aikin gyaran asibitin cikin gaggawa wanda zai hada da dawo da wutar lantarki da samar da sauran kayan aiki.
Ya kuma jinjina wa ma’aikatan lafiyan da ya tarara a bakin aiki bisa jajircewa da suka nuna wurin sauke nauyin da ke wuyarsu na kula da marasa lafiya duk rashin yanayi mai kyau da asibitin ke ciki. Inda ya sanar da yi musu kyauta domin kara musu kwazo.