Thursday, September 21, 2023
GidaDa Dumi-DumiHar yanzu Dangote ne wanda ya fi kowa kudi a Afirka –Mujallar...

Har yanzu Dangote ne wanda ya fi kowa kudi a Afirka –Mujallar BloombergMujallar Bloomberg ta kasar Amurka ta ce har yanzu babu wanda ya doke Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya kasance mutumin a kudi a nahiyar Africa duk da faduwar darajar kudin kasarsa Naira.

A cewar Mujallar cikin jerin sunayen manyan attajirai da ta saba fitarwa a kullum, a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana Dangote a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Africa da ya mallaki dala biliyan $15.6bn.


Har ila yau, kwanan nan wata Mujallar kasuwancin zamani da ke Birtaniya Richtopia, ta sanya sunan Dangote a cikin wanda suka fi kowa jinƙai a Duniya.Wannan karramawa ta biyo bayan tallafawa gidauniyarsa ta Aliko Dangote Foundation (ADF) da dala biliyan 1.25.

Attajirin ya fara aiyyukan jinkai a wannan gidauniya a shekarar 1981, da manufar bunkasa samar da sauyi a al’umma ta hanyar inganta lafiya da walwalar al’umma, samar da ingantaccen ilimi, da fadada damar karfafa tattalin arziki.

Wannan ya sa gidauniyar ta fi mayar da hankali a kan tallafawa kiwon lafiya da samar da abinci mai gina jiki tare da tallafawa fannin ilimi da agajin jin kai.

Sauran attajirai da Bloomberg ya wallafa sunayensu daga Afrika sun hada da Johann Rupert na Afirka ta Kudu da a kawanaki aka bayyana ya doke Dangote yanzu yana da dala biliyan 13.3, Nicky Oppenheimer ita ma daga Afirka ta Kudu, Nassef Sawiris na kasar Masar, Natie Kirsh shi ma daga Afirka ta Kudu, sai Naguib Sawiris daga Masar da kowannensu ya mallaki dala biliyan 9.0, dala biliyan 7.47, dala biliyan 7.37 da kuma dala biliyan 5.93.

Wadannan su ne ‘yan Afirka biyar da sunayensu ya fito a jerin attajiran duniya 500 na shekarar 2023.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments