Zakari Alfa, matashi ne da ke aiki a matsayin maigadi a jami’ar jihar Neja wato Ibrahim Badamasi Babangida University da ke girin Lapai. Ya fara wannan aikin ne da takardar shaidar kammala kwalejin horas da malamai wato NCE duk da cewa an yi ta yunkurin kashe masa gwiwa kan cewa matakin karatunsa ya fi karfin ya yi aikin gadi.
“A lokacin da na samu aikin nan, abokaina sun so su kashe min gwiwa akan cewa na fi karfin aikin, sai dai sun manta cewa babu wanda ya fi karfin abin da Allah ya kaddara masa”.

Wannan aikin dai ya baiwa Alfa damar ci gaba da karatu wanda a shekarar 2014 ya samu gurbin karatun digirin farko kuma ya kammala a shekarar 2019.
“Kafin wannan aikin, ina da burin ci gaba da karatuna, don haka aiki a matsayin maigadin jami’a ya bani wannan dama. Bayan na kammala kuma sai wani Malamina ya bani shawara da na sake dorawa da karatun digiri na biyu wannan zai fi bani damar samun aiki da wuri musamman ma a jami’ar da nake aiki.

Wannan shawara da wannan malamin ya baiwa matashin ta mishi dadi duk da girman nauyinda ke kansadawainiyar iyali; mata da ‘ya’ya uku ga kuma albashinsa bai taka kara ya karya ba. Zakari bai karaya ba, halin yanzu ya kai matakin karshe na kammala karantun digirin na biyu kamar yadda ya shaida wa majiyarmu Lapai Tv.