An zargi waliyyin wata amarya da sace mata sadaki gabanin daurin auren a unguwar Kurna da ke karamar hukumar Dala ta jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin da aka gano faruwar lamarin, an bar mutane cikin halin rashin tabbas game da daurin auren.
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
- Gawuna ne ya ci zaben gwamnan Kano-Kotu
Wani mazaunin yankin mai suna Sunusi Dan Mamman ya shaida wa maniyar hausa Daily Times cewa bayan na tsawon lokaci, mahalarta daurin auren sun amince da a caji duk wanda yake zaune kusa da inda aka sace kudin.
“A yayin binciken ne aka gano kudin a cikin aljihun waliyyinta, wanda ya ce bai san yadda suka shiga aljihunsa ba.
“Da samun kudin, sai aka kori waliyyin daga masallaci saboda ba zai iya tsayawa amaryar a matsayin wakilinta ba, maimakon shi sai aka sa kaninsa ya bada aurenta daga nan aka co gaba da sha’anin biki”.