Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da taohon shugaban kasar Muhammadu Buhari a birnin London na kasar Birtaniya.
Tinubu ya ziyarci kasar ne bayan kammala wani muhimmin taro a Faransa wanda ake ganin don ya gana da Buhari ya sa ya ziyarci kasar duk da cewa bai tsara hakan ba tun farko.

Ana sa ran a daren yau dukkansu za su koma gida domin yin Sallah da iyalansu.
Wannan dai ita ce Sallah ta farko da Bola Tinubu zai yi a matsayin Shugaban kasar.