Mahukuntan lafiya a Amurka sun tabbatar da bullar cutar Maleriya a kasar a karon farko cikin shekaru 20.
Wannan sanarwa ta fito ne bayan gano mutun hudu dauke da ke ita a jihar Florida watanni biyu da suka wuce,
BBC ta ruwaito jami’an gwamnatin jihar sun fitar da gargadi tare da jan hankalin mazauna yankin su rika tsaftar muhallinsu da amfani da gidan sauro da maganin feshi.
- Sojoji sun gano inda ake kera bindigogi a Kaduna
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
Haka kuma an fitar da irin wannan gargadi a jihar Texas.
Ana iya cewa babu zazzaɓin maleriya a Amurka ko ba kasafai ake samunta ba a kasar, akasari mutane ne ke shiga, amma masana kimiyya sun yi gargadi cewa a yanzu zazzabin na iya yaduwa saboda sauyin yanayi.
Maleriya na haddasa zazzabi mai tsanani da kasala. Kuma tana sanadin rayukan dubban mutane a duk shekara a fadin duniya.