Monday, September 25, 2023
GidaKunnen GariAttajiri ya sake faduwa jarabawar shiga jami'a karo na 27 a China

Attajiri ya sake faduwa jarabawar shiga jami’a karo na 27 a China

Wani dan kasar China, Shi Liang, ya fadi jarrabawar shiga jami’a da suke kira da  “Gaokao” a kasar a karo na 27 a bana, abin da ya sanya shi cikin shakku kan cimma burinsa na yarinta na zuwa jami’a.

Mutumin mai shekaru 56, ya samu maki 424 daga cikin jimillar maki 750 na jarabawar, wanda hakan ya yi kasa da makin da ake bukata don samun gurbin shiga kowace jami’a a kasar.

Mista Liang, wanda attajiri ne a shekarar 1983 ya rubuta jarabawar ta farko a lokacin ya na dan shekara 16, ya kuma kasance mai burin karatu a wata babbar jami’ar kasar ta Sin kamar yadda majiyarmu ta Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito.

Domin cimma wannan buri a shekarar nan, ya kaurace wa barasa, ya kuma sadaukar da sa’o’i 12 wurin yin karatu, sai dai abin takaici, mai yiwuwa ba zai sake jarrabawar ba a shekara mai zuwa, saboda rashin samun nasara a dukkan jarabawoyin da ya shafe rayuwarsa yana rubutawa.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments