Tashoshin jiragen sama 15 aka sanyawa sunayen wasu mashahuran ‘yan Najeriya.
Na yi murna da aka sanyawa filin jirgin saman Minna da ke Jihar Neja, sunan marigayi Malam Abubakar Imam, tsohon marubuci kuma ɗan jarida. Mawallafin littafin Magana Jari Ce, kuma Editan farko na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo!
- Sojoji sun gano inda ake kera bindigogi a Kaduna
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
Ba lallai sai ka zama gwanin iya rubutu da turanci ba. Ɗaukaka ta Allah ce! Na san ba za mu taɓa mantawa da gudunmawar jagoran mu Alhaji Ado Ahamad Gidan Dabino, da ya samu shaidar yabo ta ƙasa ta MON, albarkacin rubutu da harshen Hausa.
Mu daina ƙyamar yin rubutu da harshen mu na gado, don kar a raina ilimin mu da wayewarmu!
Ga su nan:
- Akure Airport – Olumuyiwa Bernard Aliu
- Benin Airport – Oba Akenzua II
- Dutse Airport – Muhammad Nuhu Sanusi
- Ebonyi Airport – Chuba Wilberforce Okadigbo
- Gombe Airport – Brigadier Zakari Maimalari
- Ibadan Airport – Samuel Ladoke Akintola
- Ilorin Airport – Gen. Tunde Idiagbon
- Kaduna Airport – Hassan Usman Katsina
- Maiduguri Airport – Gen. Mumammadu Buhari
- Makurdi Airport – Joseph Sarwuan Tarka
- MINNA AIRPORT – MALAM ABUBAKAR IMAM
- Nassarawa Airport – Sheikh Usman Dan Fodio
- Osubi Airport – Alfred Diete Spiff
- Port Harcourt Airport – Obafemi Jeremiah Awolowo
- Yola Airport – Lamido Aliyu Mustapha