Monday, September 25, 2023
GidaDa Dumi-DumiFaston da ya musulunta a watannin baya na aikin Hajjin bana

Faston da ya musulunta a watannin baya na aikin Hajjin bana

Fitaccen Malamin majami’an nan na kasar Afirika ta Kudu Pastor Abraham Richmond na daga cikin Mahajjatan bana da ke aikin sauke farali a kasa mai tsarki.

Richmond wanda sananne ne wurin jagorantar mabiya addinin Kirista a kasarsa, ya karbi Shahada don komawa addinin musulunci a watannin biyu zuwa uku da suka gabata.

Shafukan manyan malaman addinin Islama irinsu Sheikh Dr. Muhammad Salah da Dr. Zakir Naik sun ruwaito cewa a sakamakon komawa musulunci da wannanmalamin ya yi, dubban mabiyan majami’arsa suma sun karbi musulunci.

Malamin wanda ya shafe shekaru 15 yana koyarwa zuwa ga addinin kiristanci, yanada mabiya sama da dubu 100 a majami’arsa.

Hotuna da bidiyoyinsa sun bayyana cikin tufafin harami (Ihrami) yayin da yake kuka tare da godiya ga Allah da ya ganar da shi hanyar gaskiya.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments