Thursday, September 21, 2023
GidaKunnen GariYa kashe tsohuwar matarsa bayan ya samu labarin za ta sake yin...

Ya kashe tsohuwar matarsa bayan ya samu labarin za ta sake yin aure…

Muhammad Kabir Aminu

Rundunar ƴansandan jihar Adamawa sun cafke wani mutum mai kimanin shekaru 56 a duniya wanda ya bugi tsohuwar matar shi ƴar ma 38 a duniya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ta bayan ya samu labarin cewa za ta yi aure, sanadiyyar mutuwar ta kenan.

Shi dai tsohon mijin nata wanda ake zargi da aikata laifin kisan mai suna Aminu Abubakar, da ke zaune a Unguwar Lelewaji, Shagari Estate a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu an bayyana cewa ya je wurin Nana Fadimatu da misalin ƙarfe 10pm a ranar Juma’ar nan da ta gabata bayan da ya samu labarin cewa za ta yi aure.

Sun dai yi aure ne shekaru tara da suka gabata, inda suke da ɗa ɗaya kafin rabuwar su.

Yayin da suke ganawar ne hushi ya ɗebe shi inda ya riƙa dukanta da wani abu mai nauyi dake hannun shi wanda nan take ta suma daga baya kuma rai ya yi halinsa.

Yayin da wanda zai aure ta, Mahmud Rufai, da ke zaune a Unguwar Shagari Annex ya samu labarin sai ya hanzarta kai maganar ga ƴansanda na Shagari Police Division, inda suka damke wanda ake tuhumar tare da tafiya da shi offishin su.

A yanzu haka yana hannunsu, yayin da ake ci gaba da bincike.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments