Shmsuddeen Magaji Bello (Shamsuddeen Uncolonized) ya kafa tarihi na kammala Digiri na Biyu (Masters) da mataki mafi daraja wato “First Class” a jami’ar Ohio da ke kasar Amurka.
Matashin wanda dan asalin jihar Kebbi ne daga arewacin Najeriya, ya fita da maki “3.96/4” a fannin Ci gaban Kasa da Kasa wato International Developmnebt tare da samun shaidar kwarewa a fannin nazarin Tsaro da Zaman Lafiya “War and Peace Studies”.

Shamsudden Uncolonized wanda kwararren Lauya ne, ya jagoranci kungiyar Daliban Afrika.