Shahararren mawakin soyayya nan na Hausa, wanda aka fi sani da Hamisu Breaker, ya magantu game da zargin da ake masa na soyayya da jarumar Nijar, ya sanar da cewa babu wata alaƙa ta soyayya da ta taɓa shiga tsakanin sa da Rakiya Musa Poussi.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ƙarshen makon nan ne dai Hadiza Gabon, fitacciyar ƴar fim ɗin Kannyywood, a wani shirin hira-da-baƙo da take gabatarwa a tashar Arewa24, ta tattauna da Rukayya Yusuf, wacce a ka fi sani da Rakiya.
A hirar, Rakiya ta bada labarin soyayyar su da Breaker, da irin wahalar da ta sha a soyayyar, a wani yanayi mai ban tausayi, inda har ta fashe da kuka yayin bada labarin a cikin shirin.
Wannan hira ta Rakiya ta haifar da cecekuce a kafafen sadarwa, musamman ma Facebook, inda har wasu da su ka kalli shirin, ke cewa suma sai da su ka zubar da hawaye sabo da tausayi.
Sai dai kuma a wani martani da Breaker din ya yi a shafinsa na Twitter, ya ce shi bada shi ta yi wannan soyayyar da ta bada labari a shirin na Gabon ba, sai dai idan da wani can ta yi.
Ya ƙara da cewa bashi da wata alaƙa da jarumar ta soyayya sai dai ta mutumci.
“Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lafiya. Dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankalina akan wannan batun da ya ke ta yawo cewa Rukayya Yusuf ƴar Asalin Niger wadda Hadiza Aliyu tayi hira da ita wasu mutane na cewa wai dani ta yi soyayya kuma har na juya mata baya.
“Sam Sam wanna maganar ba haka take ba hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai mutunci,” in ji Breaker.