Thursday, September 21, 2023
GidaSiyasaPDP ta yi Allah wadai da kiran da APC ta yi wa...

PDP ta yi Allah wadai da kiran da APC ta yi wa INEC kan zaben gwamnan Kebbi

Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta ce kiraye-kirayen ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Kebbi da APC ke yi katsa-landan ne ga hurumin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Idan za a iya tunawa, bayan bayyana sakamakon a matsayin wanda bai kammala ba, wani jigo a jam’iyyar APC a jihar, Abubakar Garin-Malam, ya bukaci hukumar INEC da ta ayyana dan takaran APC, Dr. Nasiru Idris a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai shugaban kwamitin yada labarai na jam’iyyar PDP na jihar, Sani Dododo, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ya bayyana kiran a matsayin wani yunkuri na raina hukumar zabe ta kasa, INEC.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya, NANya ruwito Sani Dododo ya ce: “Jam’iyyar PDP ta yi watsi da kiran da Alhaji Abubakar Gari Malam, Shettiman Gwandu ya yi na bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Kebbi da ba a kammala ba, yana mai bayyana kiran a matsayin mara kan gado.

A yayin da ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici  da kuma mazarin karban mulki da APC ke yi, Dododo ya tabbatar da cewa INEC ta san me take yi kafin ta kai ga yanke hukuncin ayyana zaben gwamnan Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.

“Babu shakka cewa Abubakar Malam yana da mugun nufi a kiran da ya yi da ba kowa ya sani ba,” in ji shi.

Sai dai ya yi kira ga duk masu biyayya ga PDP da sauran jama’a da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da bin doka da oda yayin da suke jiran sanarwar hukumar INEC.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments