Thursday, September 21, 2023
GidaSiyasaKotun Daukaka Kara ta kori karar PDP akan Tinubu da Shettima

Kotun Daukaka Kara ta kori karar PDP akan Tinubu da Shettima

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori karar da jam’iyyar PDP ta shigar, inda ta nemi kotu da ta soke takarar Asiwaju Bola Tinubu da Kassim Shettima a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Jaridar Punch ta ruwaito Jam’iyyar PDP, ta bukaci kotun daukaka kara da ta janye hukuncin da mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar 13 ga watan Janairu, inda ta yi watsi da karar da ta shigar kan cewa PDP ta da hurumin shigar da karar.

A hukuncin da aka yanke a jiya Juma’a da yamma, kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara, ya yanke hukunci kan cewa PDP ta kasa kawo hujjar huruminta akan wannan kara da ta shigar. Mai shari’a James Abundaga, wanda ya amince da jawaban da lauyoyin wadanda ake kara suka yi, suka mikawa wadanda ake karan, ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin mai tsoba baki akan lamuran da basu shafeta ba.

Bayan ya kori karar tare da jaddada hukuncin Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a Abundaga ya ci lauyan PDP da ya shigar da karan Barista JO Olotu tarar zunzurutun kudi naira miliyan 5.

PDP na kalubalantar sahihancin tikitin takarar Tinubu/Shettima, inda ta ce zaben Shettima a matsayin wanda zai yi takara ya saba wa tanadin dokar kasa.

Da take ikirarin cewa Shettima na takara biyu, PDP na zargin Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa da kuma dan takarar Sanatan Borno ta tsakiya,wanda a cewarta hakan ya saba wa doka.

A nasu bangare, wadanda ake kara sun bukaci kotun da ta yi watsi da karar saboda rashin hurumin PDP a ciki. Sun yi nuni da cewa PDP bata da hurumin tsoma baki a duk hukuncin da jam’iyyar za ta yanke somin lamura ne na cikin gida.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments