Mai Alfarma Sarkin Musumi Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya.
Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar ne ya tabbatar da haka a jawabin gann wata da ya yi wa manema labarai a Fadarsa da ke Sokoto, indaya ce ya samu tabbacin ganin watan ne daga fadin Najeriya.
Tun da farko Hausa Daily Times ta ruwaito garuruwan da aka ga watan sun hadar da Suleja, Minna da Kontagora da ke jihar Neja, sai Babban Birnin Tarayya Abuja da Birnin Kebbi da kuma jihar Sokoto da kuma birnin Lagos.
“Gobe Alhamis 23 ga watan Maris na shekarar 2023 zai zama daya ga watana Ramadan, Hijira 1444”. A cewar sanarwar.