Kwamitin duban wata na kasar Saudiyya ya sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Ramadan ba a kasar.
Cikin wata sanarwa da shafin Haramain Sharifain na kasar ya fitar a yau Talata, ya ce “ba a ga watan Ramadan ba yau, sabodahaka ranar Alhamis 23 ga watan Maris, 2023 zai kasance daya ga watan Ramadan, Hijira1444.
Ya kara da cewa, daga gobe Laraba za a fara gudanar da Sallar Tarawihi (Asham) a masallatan Haramin Makkah da Madina.