Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin Najeriya da su fita yau Talata 29 ga watan Sha’aban wanda ya yi dai dai da 21 ga watan Maris, 2023 domin fara duba jinjirin watan Ramadan.
Cikin wata takardar sanarwa da Shugaban Kwamitin Harkokin Addinai na fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar, an kuma umarci al’umma da su sanar da Hakimi ko Dagacin mafi kusa da su idan sun ga watan da idanun su domin a sanar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi cikin lokaci.
Tuni dai sauran wasu kasashe a sassan duniya ciki har da Saudi Arabia suka sanar da fara duna watan suma a yau Talata.