Hukumar zabe a Adamawa INEC ta sanar da dage sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa zuwa karfe 12 ranar Litinin domin daura sakamkon zaben a shafin intanet na INEC.
Tun da farko, jami’an PDP a jihar na zargin Kwamishinan Zaben INEC na jihar Hudu Yunusa, da yunkurin sauya sakamakon zabe daga na asali, wanda a dalilin hakan suke ganin sauya sakamakon zai kada dan takaransu wato gwamna mai ci Ahmadu Umaru Fintiri domin a baiwa Sanata Aisha Dahiru Binani na APC damar yin nasara.
Sakamakon kananan hukumomi 20 ne aka sanar cikin kananan hukumomi 21 da ke jihar, wanda ya rage na karamar hukumar Fufore ne ake rigima akai. Sakamkon ya nuna gwamnan jihar ne ke kan gaba.
An ga wani jami’in PDP wanda ya tashi yana fade-fade tare da nuna dan yatsa ga Kwamishinan zaben jihar a cibiyar tattara zaben jihar da ke birnin Yola, cikin harshe ingiliahi yana cewa “ba mu yadda da wannan Kwamishinan zaben ba domin shi ne ya haifar da duk abin da ake ciki a halin yanzu”.
Jami’in na PDP yi kira ga duniya da ta san halin da jihar ke ciki domin duk abin da ya faru a Adamawa shi ne ya haddasa. Ya kuma yi zargi da wani nadadden faifan tattaumawar waya da aka fitar, an ji Kwamiahnan INEC dim yana sanar da Baturen Zaben karamar hukumar Fufore da ya yi duk yadda zai yi ya sauya sakamakon zaben domin Sanata Binani ta yi nasara.