Tuesday, September 26, 2023
GidaSiyasaAna ƙoƙarin maimaita abin da aka yi mana a zaben 2019, Kwankwaso...

Ana ƙoƙarin maimaita abin da aka yi mana a zaben 2019, Kwankwaso ya yi zargi

Jagoran jam’iyyar NNPP Rabi’u Kwankwaso, ya nuna rashin amincewar sa da yunkurin da ake yi na ayyana zaben gwamnan jihar Kano a matsayin wanda bai kammala ba wato “inconclusive”.

A yayin ganawa ‘yan jarida da sanyin safiyar yau Litinin a harabar Ofishin Hukumar Zabe a kano, Kwankwaso ya yi kira ga hukumar INEC da ta yi abin da ya dace domin jam’iyyarsa ce ke kan gaba a zaben.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya nemi da da a yi musu gaakiya da adalci don gudun kowane irin rigima bayan ayyana sakamakon zaben duk da ba zai so ba.

Bisa alkaluman sakamakon zaben dai, dan takaran jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf ne kan gaba yayin da na APC Nasiru Yusuf Gawuna ke biye da shi.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments