Sa’o’i bayan hukumar INEC ta ayyana dan takaran jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Kano, jam’iyyar APC a jihar ta bukaci magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu saboda tsokanar da ake zargin ‘ya’yan jam’iyyar NNPP ke musu.
Rahotanni sun ce ‘ya’yan jam’iyyar NNPP da ke murnar samun nasara zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, sun kai hari tare da lalata dukiyoyin wasu magoya bayan jam’iyyar APC a jihar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda daya daga cikin wadanda hasarar ta shafa har da mawakin jam’iyyar APC Dauda Kahutu Rarara, inda aka kai hari gidansa, tare da kona motoci a gidan. .
Kwamishinan yada labarai jihar, Malam Muhammad Garba, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa masu jajircewa da aminci ga jam’iyyar.
“Jam’iyyar APC na nazari sosai kan yadda zaben ya gudana da kuma aka tattara sakamakon zabe da nufin yanke shawara a lokacin da ya dace,” inji shi.