Sashe na Uku na rundinar hadin gwiwa na Operation Hadin Kai a garin Monguno da ke jihar Borno ya gudanar da gasar kur’ani ga matasa domin inganta alakar sojoji da fararen hula.
Wata sanarwa da mai magana da yawun sashen Babatunde Zubairu ya fitar a ranar Juma’a ta ce kwamandan sashen na 111, A.E Abubakar ne ya shirya gasar irinta na farko da nufin karfafa goyon bayan al’ummomin da suke zaune a yankunansu domin dorewar nasara da ake ci gaban yaki da ‘yan tada kayar baya.
Kamfanin Dillancin Labarun Najeriya, Mista Abubakar ya ce gasar tunani ne na babban kwamandan rundinar Operation Hadin Kai, I.S Ali, wanda ya dauki nauyin gasar. Ya ce Kwamanda Ali, ya kirkiro da wannan hanyar ne domin kara karfafa mu’amala tsakanin sojoji da al’umma.
Mista Ali ya ce gasar za ta kara wayar da kan matasa kan hakikanin koyarwar Musulunci, wanda ke kawo zaman lafiya. Ya bukaci karin hadin kai da hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Borno da ma yankin baki daya.
A nasa sakon, Gwamna Babagana Zulum, wanda mataimakin shugaban karamar hukumar Monguno, Sanda Modu ya wakilta, ya yaba wa rundunar sojin bisa wannan shiri da sauran ingantattun matakan da aka dauka kawo yanzu domin samun nasara a yaki da masu tayar da kayar baya.
Ya yaba wa babban hafsan hafsoshin sojin kasar bisa sabon alkawarin da ya dauka na yaki da ‘yan tada kayar baya tare da tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da tallafi a wannan bangaren.
A yayin taron an gabatar da kyautar kujerar Umrah ga wanda ya lashe gasar, Muhammed-Nur Mustapha, sai kuma N300,000 da N200,000 ga Zaharadeen Yusuf da Mohammed Ali wanda ya zo na biyu da na uku.