Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da cewa ba gaskiya bane labarin da ke yawo kan cewa za ta gudanar da zaben mazabun da aka ayyana da “basu bammalu ba” (inconclusive) rana da na gwamna da ‘yan majalisun jihohi da za a yi gobe.
Cikin wata takardar sanarwa da Kwamishinan Hukumar na kasa mai kula fannin yada labarai da ilimantar da masu zabe Festus Okye, hukumar ta ce zaben daban za a yi shi ba za a hada da na gwamnoni ba.
Ta yi bayani da cewa, da farko ta daga zaben kujerar Sanatan Gabashin jihar Enugu wanda ya dace a a gudanar tare da na Shugabankasa a ranar 25 ga watan Feburairun da ya gabata, sai dai an daga din ne domin baiwa jam’iyyar LP damar gudanar da sabon zaben fidda gwani domin maye-gurbin dan takararta da ya mutu kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Sai kuma na biyu da ta yi bayani da cewa, akwai zaben kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Esan Central/Esan West da Igueben a jihar Edo, shi ma an daga ne bisa matsalar da aka samu a wurin buga takardun kuri’a, wanda shima sabon zabe ne za a yi.
Ta nemi al’umma da su yi watsi da duk wani labari da ake yadawa sabanin wannan, inda ta kira da labarin ‘kanzon kurege.
Jihohi da dama ne za a sake gudanar da zaben ‘yan majalisar Dattawa da na Wakilai bisa rashin kammaluwansa irin su Sokoto Kebbi, Zamfara da dai sauransu.