Wata ma’aikaciyar jinya a asibitin Kwararru na Ahmed Sani Yariman Bakura da ke jihar Zamfara, Asma’u Lawali Bungudu, ta rasu bayan da ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take tsaka da aikin duba marasa lafiya.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa ma’aikaciyar jinyar ta kasance cikin koshin lafiya. lokacin da ta isa asibitin domin aiki da sanyin safiyar Laraba amma an tabbatar da mutuwarta sa’o’i kadan bayan ta kama aiki.
Kakakin asibitin, Auwal Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya sanar da cewa Asma’u na kan aikinta, kuma ta duba marasa lafiya kusan 30 kafin ta sanar da likita game da abin da take ji a jikinta.
Da yake karin haske, Kakakin asibitin ya ce bayan korafin nata, nan take ta yanke jiki ta fadi, inda likitoci suka garzaya domin ceto ta.
“Likitoci sun yi iya kokarinsu don ceto rayuwarta amma hakan ya ci tura domin rai ya yi halinsa nan take,” in ji shi.
A cewar Usman, tuni hukumar gudanarwar asibitin sun mika gawar ga ‘yan uwan marigayiyar.
Da aka tuntubi ‘yan uwan marigayiyar sun tabbatar da cewa Asmau ta bar gida cikin walwala da koshin lafiya da sanyin safiyar Laraba zuwa asibiti da take aikin jinya ba tare da wani korafin rashin lafiya ba.