Wata mahaifiya mai shayarwa ta jefar da jaririnta yayin da take gudun ceton rai daga ‘yan daba wadanda, bayan sun mamaye unguwarsu a Minna, fadar jihar Neja.
Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a makon jiya a unguwar Gbeganu, inda ‘yan daban ayari guda suka afkawa mazauna unguwar tare da fasa shaguna.
Matar wadda ke kokarin tserewa daga batagarin, ta yi watsi da jaririn ne yayin ya fadi daga hannunta.
Tuni dai ‘yan banga da wasu kungiyoyin tsaron sa kai tare da taimakon wani mai gidan Blo a unguwar Malam Abdullahi Ibrahim, suka ceto yaron tare da kai shi asibiti wanda kuma bayanai suka tabbatar yana ciki koshin lafiya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ‘yan sanda ba su mayar da martani game da wannan abin da ya faru ba.
Har yanzu birnin Minna dai na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro daga adannan gungun batagari, wadanda ke addabar ciki da wajen birnin baya ga ‘yan ta’adda da ke ci gaba da farwa al’ummomin da ke wasu daga cikin garuruwa da kauyukan da ke jihar ta Neja.