Tuesday, September 26, 2023
GidaNomaMasana sun gargadi manoma game da shukar wuri a daminar bana

Masana sun gargadi manoma game da shukar wuri a daminar bana

Babban Darakta na Cibiyar Binciken hatsi ta kasa (NCRI), Badeggi da ke a jihar Neja, Dakta Aliyu Umar, ya shawarci manoma da kada su yi gaggawar yin shuka a ruwan saman farko.

Umar ya bada shawarar ne a wata hira da manema labarai a garin Bida a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa, saboda abin da aka shuka a farkon saukan ruwan sama na iya konewa sakamakon zafi, idan ruwan sama bai ci gaba ba.

Babban daraktan hukumar ta NCRI ya ce domin gudun asara, manoma su jira wani ruwan sama kafin su shuka amfanin gona.

Ya bayyana cewa saukan ruwan sama da wuri da aka samu alama ce ta damina mai kyau a fadin kasar nan, amma ya gargadi manoma da kada su yi gaggawar yin shuka.

“Idan kowane manomi yana son yin amfani da wannan ruwan sama na farko don shuka, irin wannan manomi ya kamata ya tabbatar da tanadin isasshen ruwan da zai shayar da amfanin gonakinsa idan ruwan sama bai ci gaba ba.

“Bai kamata a yi shuka a damina ta farko ba, amma manoma su shirya gonakinsu kafin damina ta sauka da kyau.

“Damina ta farko tana nufin lokaci ya yi da manoma za su fara share gonakinsu amma ba su yi shuka ba.

Ya kara da cewa, “Ba yana nufin su fara shuka nan da nan ba, yana nufin su shirya kasa su fara shiri kafin damina ta kankama.”

Umar ya kuma shawarci manoma da su rungumi noman gauraye saboda alfanunsa.

“Ina so in ba manoma shawara su shuka abubuwa da yawa yadda idan wani abu ya faru, asarar za ta yi kadan,” in ji shi.

Ya kuma bukaci manoma da su rika siyan kayayyakin noma daga sanannu masu inganci don gudun kada su yi asarar kudadensu wajen gurbatattun kayayyakin aikin gona, wadanda suke karuwa a kasuwanni.

Babban daraktan ya bada tabbacin hukumar ta NCRI za ta ci gaba da samar da iri mai inganci domin bunkasa noma da samar da abinci a kasar nan.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments