Fitacciyar mawaĆ™iyar nan Binta Labaran wadda aka fi sani da Fati Nijar ta koka kan yadda ta ce an gama shan wahala da su a tallan ‘yan siyasa amma daga bisani aka yi watsi da su aka dauko wasu da suka zo daga baya aka rike.
Ta bayyana hakan ne a wani gajeren bidiyon da ta wallafa a shafinta na TikTok, inda ta ce muddin mutum bai yi a hankali ba sai Ć´an siyasa sun kai shi sun baro shi.
Ta yi bayani da cewa, sun sha wahala lungu da saƙo suna tallan wasu ƴan takara amma ta je gidan ɗaya daga ciki an hana ta ganinsa.
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
- Gawuna ne ya ci zaben gwamnan Kano-Kotu
Ta ci gaba da cewa, gani ta yi kawai ana yi da waÉ—anda suka zo a bayan-bayansu an ajiye su da suka sha wahala a gefe, wadanda ake yi da su ba su san ma wahalar da aka sha a baya ba.
Jarumar ta kuma ce, a jira za ta yi hira inda a nan ne za ta fayyace abubuwa da dama.
Gidan Radion Freedom da ke Kano ya ruwaito cewa, maganganun mawakiyar ba zai rasa nasaba da dawowar mawaĆ™i Dauda Kahutu Rarara da jama’arsa tafiyar ĆŠan Takarar Gwamnan Kano a APC ba, wanda a baya Jaruma Fati Nijar ta yi suna wajen tallan shi lokacin da Rarara ke tafiyar Sha’aban Sharada.