Tuesday, September 26, 2023
GidaKasuwanciEmefiele ya tabbatar min bankuna za su fara karba da bada tsoffin...

Emefiele ya tabbatar min bankuna za su fara karba da bada tsoffin kudi- Gwamna Soludo

Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Charles Soludo ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankuna da su fitar da tsofaffin takardun kudi na naira.

Soludo ya ce gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele ne ya bayyana masa hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho a daren Lahadi.

Soludo ya ce “Babban Bankin ne ya umurci bankunan kasuwanci da su ba da tsofaffin takardun kudi tare da karbar tsoffin kudaden idan aka kawo musu na ajiya daga abokan ciniki,” in ji Soludo.

“Ma’aikatan bankunan kasuwanci su samar da lambobin ajiya kuma babu iyaka ga adadin lokutan da mutum ko kamfani zai iya yin ajiya.”

Soludo, wanda tsohon gwamnan CBN din ne, ya ce Emefiele ya bayar da umarni a taron kwamitin bankunan da aka gudanar a ranar Lahadi, 12 ga Maris, 2023 cewa bankunan su fitar da tsofaffin takardun kudi na naira.

Kamar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Dapo Abiodun na jihar Ogun da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, Soludo ya bukaci mazauna Anambra da su “karba tare da gudanar da harkokin sana’o’insu cikin walwala da tsofaffin takardun kudi (N200; N500; da N1,000) da kuma sabbin takardun kudin”.

Bayanan gwamnan Anambra na zuwa ne kwanaki 10 bayan da Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa tsofaffin takardun kudi 500 da 1000 za su ci gaba da zama a kan doka har zuwa karshen Disamba 2023.

Kafin yanke hukuncin kotun, CBN ya sanar da ‘yan Najeriya cewa tsoffin takardun kudin naira ya daina shiga kasuwa tun ranar Juma’a 10 ga watan Fabrairu.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments