Thursday, September 21, 2023
GidaDa Dumi-DumiCBN ya tabbatar da cewa za a ci gaba da karban tsoffin...

CBN ya tabbatar da cewa za a ci gaba da karban tsoffin takardun kudi har karshen 2023

Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar Litinin ya ce tsofaffin takardun na N200, N500, N1,000 za su ci gaba da kasancewa halastattu domin hada-hadar kasuwanci har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

Mukaddashin Daraktan Sadarwa na Babban Bankin, Isa AbdulMumin ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin. Hakan dai na zuwa ne kwanaki 10 bayan da kotun kolin ta yanke hukunci da cewa a ci gana da amfani da tsoffin takardun kudi tare da sabbi har zuwa karshen shekara.

A ranar 3 ga watan Maris ne babbar kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da aiki da tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

Hakan ya faru ne bayan da jihohi 16 sun shigar da kara domin kalubalantar matsayar gwamnatin tarayya na hana amfani da kudin.

Jihohi 16 karkashin jagorancin Kaduna, Kogi da Zamfara sun ganatar wa kotun kolin da bukatar neman ta yi watsi da manufofin gwamnatin tarw da cewa ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba na wahala.

Daga nan ne kotun kolin ta ce rashin bin umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar 8 ga watan Fabrairu alama ce ta kama-karya, inda ta kara da cewa shugaban ya saba wa kundin tsarin mulkin tarayya ta yadda ya bayar da umarnin sake canza fasalin Naira da CBN ya yi.

Sai dai fadar shugaban kasa ta magantu dangane da zargin da ake mata na hana CBN bin umarnin kotu, inda a ranar Litinin ta ce shugaban kasa bai taba fadawa CBN da ofishin Ministan Shari’a da cewa kada su bi umarnin kotun koli ba.

“CBN ba ta da wani dalili na kin bin umarnin kotu bisa uzurin jiran umarni daga shugaban kasa,” in ji fadar shugaban kasa.

Fadar shugaban kasar ta kuma ce shugaban kasa cikakken mai mutunta doka ne.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments