Tuesday, September 26, 2023
GidaDa Dumi-DumiAbin da Shugaban Hukumar INEC ya ce wa lauyoyin Peter Obi

Abin da Shugaban Hukumar INEC ya ce wa lauyoyin Peter Obi

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a yau ya gana da tawagar lauyoyin jam’iyyar LP dangane da batun kalubalantar sakamakon zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Feburairu da ya gabata, wanda ya baiwa Bola Ahmed Tinubu nasarar lashe zaben.

A yayin ganawar tasu, Farfesa Mahmud ya tabbatar wa da lauyoyin jam’iyyar cewa Hukumar za ta bayar da dukkan takardun da suka bukata domin su je su gabatar wa da kotu.

Ya ce: “INEC ba ta da wani abin boyewa. Za a ba da dukkan takaddun da ke  shalkwatar Hukumar nan take. Za mu gana da kwamishinonin zabe a yau kuma za mu tattauna yadda za a baku sauran takardu da ke a matakin jiha cikin gaggawa.

Tawagar Lauyoyin Jam’iyyar Labour ta kasance a hedikwatar INEC ne don tattauna hanyoyin da za a bi domin samun takardun wadanda suke so su yi amfani da su a matsayin hajja a gaban kotu.

Jam’iyyar dai na zargin hukumar ta yi wa dan takararta magudi ne bayan ya lashe zabe, inda ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na APC a matsayin shi ne ya yi nasara.

A dayan bangare ita ma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ma na zargin dan takararta Atiku Abubakar ne ya lashe zaben.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments