Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da ya daina magana yayin da yake cikin mayen barasa.
Wike ya bayyana a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a karamar hukumar Emohua da ke jihar Ribas a ranar Juma’a, cewa yana shan ajiyayyen barasa dan shekara 40, a lokacin da yake kallon ‘yan jam’iyyarsa a talabijin suna zanga-zangar adawa da zaben shugaban kasa da aka gudanar a Abuja ranar 25 ga watan Fabrairu.
- Sojoji sun gano inda ake kera bindigogi a Kaduna
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
“Yayin da suke zanga-zangar, sai na kira wasu abokaina na bude mana barasa mai shekara 40 muna sha ina kallon zanga-zangar,” inji Wike.
A wata sanarwa da ta fita a ranar Lahadi, mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa na Atiku, Mista Phrank Shaibu, ya shawarci Wike da ya daina shaye-shaye domin ba wai “ta shafi muryarsa da dabi’unsa ne kadai ba, har ma da tunaninsa”.
“Gwamna Wike ya tabbatar da abin da muka sani cewa shi mashayi ne. Zanga-zangar da Waziri Atiku Abubakar ya jagoranta a ranar Litinin 6 ga Maris, 2023, ta nuna adawa magudin zabe da aka yi wa al’ummar Najeriya, wanda ita kanta ta kasance abin alfahari.

“Domin karin haske, zanga-zangar ta faru ne da misalin karfe 11:30 na safe. Gwamna Wike ya ce yana shan wiski yayin zanga-zangar da karfe 11:30 na safiyar ranar Litinin. Wannan ya bayyana irin mutumin da ya yi watsi da aikinsa a ranar Litinin da safe ya buge da shan barasa.
“Wannan ya bayyana dalilin da yasa muryarsa ta dishe. A bayyane yake cewa Gwamna Wike yana rawa a cikin maye. Ba shakka, shi ya sa ake siffanta shi da rashin mutunci.
Ka’ida ce ta gama gari cewa ba za ku sha kayan maye kuma ku tuƙi ba. Sai dai abin takaicin shi ne mashayi ne ke tafiyar da harkokin mulki a jihar Ribas. Wannan ya fi tayar da hankali saboda ya auri alkali. Lallai, doka ba za ta yi tasiri a gurin mashayi ba.”
Shaibu ya karyata cewa haushin Wike ba shi da alaka da tabbatar da cewa kudancin kasar ne ya samar da shugaban kasa.
Ya bayar da hujjar cewa Wike ya kasance mai rauni ne kawai wanda ya yaudari wasu mambobin tafiyarsu ta (G5) wadamda a yanzu haka suke fama da barazanar dakuahewa a siyasa.
Wike bai yi taro ko sau daya da mambobinsa na G5 ba, ya watsar da su tun bayan shan kaye da suka yi. Ya yi ta murnar sakamakon zaben duk da cewa mutanensa sun sha kaye. Wannan shi ne irin mutumin da yake, amma duk da haka ya yi ikirarin cewa ba ya aikata laifukan cin zarafin jam’iyya.”
Ya yabawa ‘yan Najeriya kusan 300,000 da suka rattaba hannu kan wata takardar koke kan domin neman Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai su kakaba masa takunkumin shiga kasar.