Tuesday, September 26, 2023
GidaSiyasaAinihin dalilin da ya sa ban goyi bayan neman Shugabancin Obi ba...

Ainihin dalilin da ya sa ban goyi bayan neman Shugabancin Obi ba – Gwamna Wike

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce bai goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Mista Peter Obi karara ba a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu saboda babu wanda ya tattauna da shi kan shugabancin Igbo.

A  cewar NAN, Sakataren Yada Labarai kungiyar Ohaneze Ndigbo Worldwide, Dr Alex Ogbonnia a cikin wata sanrawa, ya bayyana a ranar Juma’a a Enugu cewa Wike ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar ta yi da shi a Fatakwal a ranar Alhamis.

Ogbonnia ya bayyana cewa, a wajen taron, kungiyar ta fuskanci Wike a kan dalilin da ya yi ya ki marawa Obi baya a yayin zaben shugaban kasa.

Gwamna Wike zaune a fadar gwamnatin jihar Rivers.

Ya bayyana cewa Gwamna Wike ya yi mamakin yadda Ohanaeze ta biyoshi domin sanin gaskiya game rawar da ya taka wurin rashin nasarar Obi a zaben shugaban kasa.

A cewar Ogbonnia, gwamnan Rivers ya bayyana cewa kungiyar gwamnonin kudu sun fara ganawa a Asaba inda suka amince cewa mulki ya koma Kudu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa.

Ya ci gaba da cewa daga baya gwamnonin sun hadu a Enugu a watan Satumbar 2021 domin jaddada matsayar su na komawar mulki Kudu.

Ya kara da cewa a duk tarukan da aka yi, “ba a tana tattauna batun shugabanci ya koma yankin Kudu maso Gabas ba”.

Wike ya kuma bayyana cewa a cikin gwagwarmayar siyasarsa, ya yi iya kokarinsa wajen ganin bai sauka daga kan matsayar gwamnonin Kudu ba.

Wike ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP, wasu sanannun mutanen Kudu maso Gabas su ka ci amanarsa tare da yi wa ‘yan Kudu zagon kasa ta hanyar zaben dan takarar da ya fito daga yankin Arewa.

Ya kara da cewa rashin amincewar da ya yi wa yankin Kudu ne ya sa “ya samar wa Obi kayan aiki a lokacin da ya je Ribas domin yakin neman zaben shugaban kasa” yayin da ya ki bayar da ko da filin taro ne a lokacin da Atiku Abubakar ya je jihar yakin neman zabe.

Gwamnan ya ci gaba da cewa “abin da ke yawo a shafukan sada zumunta aikin hannun abokan adawar Wike ne.”

“Ni mutum ne mai jajircewa kan hukuncin da na yanke, kuma ba ni da dalilin yin karya ko kuma neman gafarar kowa.

Ogbonnia ya ruwaito Wike yana cewa “A shirye nake a ko da yaushe na kare matakaina a kowace rana kuma a kowane lokaci, kuma ban yi wa Obi ba a zaben Shugaban kasa.”

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments