Tuesday, September 26, 2023
GidaSiyasaYaudara ce abin da Obi ke son yi a jihar Anambra- Gwamna...

Yaudara ce abin da Obi ke son yi a jihar Anambra- Gwamna Soludo

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya mayar da martani ga kiran da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi na jama’ar jihar da su zabi ‘yan takarar jam’iyyarsa a majalisar dokoki dake tafe.

Obi a ranar Juma’a da ta gabata daddare ya gana da ‘yan takarar majalisar kasa da na jiha ‘yan jam’iyyar LP a Anambra, yayin da ya bukaci ‘yan takarar majalisar da su yi aiki da Soludo yayin zabe.

Obi ya ce Soludo ya kasance dan uwansa, don haka kada ya ji tsoron tsige shi idan ‘yan jam’iyyar LP sun mamaye majalisar dokokin jihar, domin abin da ya fi dacewa shi ne kawo ci gaba a jihar.

Sai dai Soludo da yake mayar da martani kan kiran, ta bakin sakataren yada labaransa, Mista Chris Aburime, ya ce kiran na yaudara ne, kuma ana son shu ka wa Soludo wani tuggu ne.

Ya ce: “Wannan kiran na da nufin yaudarar mutanen Anambra ne. Obi bai isa ya yi magana game da ci gaba a Anambra ba kuma balle ya nemi ‘yan Anambra su zabi ‘yan majalisa daga jam’iyyarsa ta adawa don yin aiki da Soludo.

“Ya yi aiki da majalisar da ‘yan majalisar dokokin da ‘yan PDP ne suka mamaye, a lokacin da ya fara zama gwamna, kuma ya san bai ji da sauki ba.

“Ya kuma sha wahala a lokacin da aka yi ta yunkurin tsige shi saboda hakan, muna fatan ba irin abin da yake son kafa wa Soludo ba ne.

“Ya kamata jama’ar Anambra su fita a ranar Asabar mai zuwa su zabi jam’iyyar APGA, idan har suna son aiyyukan ci gaba da Gwamna ya faro su ci gaba.

Soludo da Obi suna takun-saka ne kan zaben ‘yan majalisar dokokin jihar Anambra da ke tafe a mako mai zuwa.

Duk da cewa ba za a yi zaben gwamna a jihar ba, Soludo yana fafutukar samun rinjaye, idan bai samu duka ‘yan majalisar dokikin su 30 ba, yayin da Obi ke son tabbatar da kansa ta hanyar amfani da tasirinsa na haifar da yawan ‘yan majalisa a majalisar.

Obi dai a zaben shugaban kasa da aka gudanar makonni biyu da suka gabata, ya samu kusan kashi 92 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada a jihar Anambra, lamarin da ya nuna cewa ya yi nasara a jihar.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments