‘Yan ta’adda sun kashe akalla mutum shida, ciki har da wata mata mai juna biyu a Ζ™ananan hukumomin Rafi da Wushishi na jihar Neja.
Bayanai sun ce an yi garkuwa da mutane sama da mutum 50 tsakanin ranakun Talata da Laraba.
Jaridar Daily Trust da Vanguard sun ruwaito ‘yan bindigar sun yi wa al’ummomin Yakila da Hana-wanka da kuma Kundu Ζ™awanya har zuwa wayewar garin Laraba.
Sai dai mazauna garuruwan sun ce daga baya dakarun sojin sama ta Najeriya sun kawo musu Ι—auki, inda suka Ι—auki sa’o’i da dama suna artabu da ‘yan bindigar kafin su fatattakesu.
Har ila yau, mazauna garin sun ce an kashe wasu ne lokacin da ake artabu tsakanin ‘yan bindigar da kuma sojojin ta jirgin sama.
Sun kuma ce an Ι—auki gawarwakin waΙ—anda aka kashe zuwa Minna babban birnin jihar a safiyar ranar Laraba.