Tuesday, September 26, 2023
GidaSiyasaINEC ta ce sai an sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa

INEC ta ce sai an sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa

Hukumar zaɓe INEC ta ce ba wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu na kujerar majalisar wakilai ta tarayya ta mazaɓar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano.

A yau Laraba ne jami’in bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar da haka, tare da cewa za a sake zaɓen a wasu runfuna 13.

Tun da farko an bayyana Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilan ta Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Sai dai kuma bayan da hukumar zaɓen ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓukan majalisun tarayya da aka yi ranar, ba ta sanya sunansa ba a don haka ba ta ba shi takardar shedar cin zaɓen ba.

Rahotanni sun ce an kashe aƙalla mutum biyu lokacin da aka kunna wuta a hedikwatar jam’iyyar hamayya ta NNPP a yankin.

‘Yan sanda sun gurfanar da dan majalisar a gaban kotun majistare, wadda ta tura shi gidan waƙafi.

Amma kuma wata kotun tarayya ta bayar da belinsa bisa dalilin cewa laifukan da ake zarginsa da su sun haɗa da kisan kai da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba saboda haka kotun majisatre ba ta da damar da za ta tura shi zaman waƙafi.

A ranar 6 ga watan nan na Maris ne Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa ya bayar da belinsa a kan kuɗi naira mliyan 500.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments