Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala shirye-shiryen dage zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 11 ga watan Maris.
Yanzu dai an dage zaben da mako guda zuwa ranar 18 ga watan Maris na 2023 da muke ciki, kamar yadda majiya mai tushe daga hukumar ta shaida wa jaridar Daily Trust.
An bayyana cewa, dage zaben ya biyo bayan gazawar hukumar wurin sake saita na’urorin tantance masu kada kuri’a (BVAS) da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, domin samun damar yin amfani da su a zaben jihahohin.
Majiya mai tushe ta ce hukumar na gudanar da wani taro a halin yanzu, inda ta ke nazarin ko dai ranar 18 ko 25 ga watan Maris za a sanya domin gudanar da zaben.
Sai dai an samu labarin cewa an zabi ranar 18 ga Maris.