Thursday, September 21, 2023
GidaSiyasaINEC ta cire sunan Doguwa daga cikin zaɓaɓɓun 'yan majalisu

INEC ta cire sunan Doguwa daga cikin zaɓaɓɓun ‘yan majalisu

Hukumar zaɓen ta INEC ta cire sunan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa daga cikin jerin sunayen zaɓaɓɓeun ‘yan majalisar wakilan tarayya da suka yi nasara a zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu.

BBC ta ruwaito Hukumar zaɓen ce dai tun da farko ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano.

Jami’in tattara sakamakon zaɓen Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya bayyana cewa Doguwa na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’a 39,732, inda abokin takararsa na jam’iyyar NNPP Yushau Salisu Abdullahi ya samu ƙuri’a 34,798.

To sai dai a jerin sunayen zaɓaɓɓun ‘yan majalisun da hukumar zaɓen ta fitar a shafinta na Twitter, babu sunan Alhassan Ado Doguwa a cikin jerin ‘yan majalisun.

INEC ɗin ta ce an tilasta wa jami’in tattara sakamakon zaɓen wajen bayyana sakamakon da ya bai wa Doguwa nasara a zaɓen da aka gudanar.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments