A shekarar 1988 ne Kashim ya auriuwargidansa Nana Alkali a lokacin ya kammala karatunsa na jami’a kenan zai tafi bautar kasa (NYSC). Daga ita har shi ba wanda ya san me zai zama a gaba. Da dadi da wuya suna tare.
Yau shekaru 34 kenan da aurensu, yanzu shi ne zababben mataimakin shugaban kasar Najeriya, ita ce mace ta biyu a Najeriya.
Shekaru 16 da suka gabata, Kashim ya kasance Manajan Bankin Zenith reshen Maiduguri, bai yie mafarkin kai wannan matsayi cikin kankanin lokaci ba.

Darasi na Rayuwa: Mata kar ku kore shi idan ya zo da batun aure yanzu saboda abin da raina abin da yake samu. Ku amince da shi in har mutumin kirki ne kuma yana da dan abin yin da abin da kw shigo masa zai sa ya iya rikeku.
Mahmud Lamin