Thursday, September 21, 2023
GidaDa Dumi-DumiBankunan da suka bi umarnin kotu suka fara biyan tsofaffin kudade

Bankunan da suka bi umarnin kotu suka fara biyan tsofaffin kudade

Bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, wadda ta kara wa’adin dokar sauya fasalin kudin Najeriya zuwa ranar 31 ga watan Disamba, wasu bankunan Najeriya sun fara biyan tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000 ga kwastomominsu.

A yau Litinin an tabbatar da cewa bankin GT (Guaranty Trust Bank) da Polaris da wasu bankuna sun fara bayar da tsofaffin takardun kudi a Abuja da Kano.

An ruwaito wani ma’aikacin banki da ya zanta da jaridar Daily Trust yana cewa umurnin fara biyan tsofaffin kudaden da ke cikin asusunsu ya fito ne daga hukumar bankin.

Sai dai ta kara da cewa, “Matsala daya ce yanzu, ita ce karbar tsofaffin takardun kudin daga hannun kwastomomi dole sai an bukaci fom na CBN saboda ba mu da wani umarni game da hakan.”

A halin da ake ciki dai, CBN har Shugaban kasa babu wanda ya fitar da wata sanarwa a hukumance na tabbatar da bin umarnin kotun.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma’a ne kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro, ya bayyana cewa umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa Babban Banki Kasa CBN na daina amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000, ba tare da tuntubar jihohin da Majalisar Tarayya da ta jihohi da sauran masu ruwa da tsaki ba, a matsayin saba wa kundin tsarin mulki.

Kotun kolin ta lura cewa ba a ba da sanarwar da ta dace ba kafin aiwatar da manufar kamar yadda dokar CBN ta tanada.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments