Wani matashi mai suna Umar Sani da ya auri mata biyu a rana guda a garin Minna na jihar Neja, ya ce yana ji kamar yana aljanna.
Sani, wanda ya auri Safiyya Tanimu Nasidi da Maryam Yusuf Galadima a ranar Juma’a, ya shaida wa Shafin Tsalle Daya cewa “Ina ji kamar an ba ni gida a aljanna, ina godiya ga Allah matuka sannan ina cikin fari ciki mara misaltuwa.
“Na gode wa Allah da ya cika min burina na auri mata biyu a rana daya. Dukansu kuma suna da fahimta. Ina matukar godiya da hakan.
“Mutane da yawa sun yi tunanin cewa za a sami matsala daga ɗayansu, amma Allah cikin hikimarsa, ya sa aka yi komai lafiya.”
Umar ya bayyana cewa ya kudiri yin hakan ne saboda ya taso a gidan da ya tarar da mata fiye da daya.
“Tun ina ɗan shekara 10, na ga mahaifina yana da mata huɗu kuma na ga yadda suke zaman lafiya. Na yi wa kaina alkawari zan auri mata fiye da daya idan na samu hanya, ko in yi aure uku ko hudu a rana guda”.
Ko da yake ya ce iyayensa sun yi mamakin shawarar, amma ba su hana shi cika burinsa ba.
“Iyayena sun yi mamaki domin ko mahaifina bai auri mata biyu a rana daya ba. Amma ba su yi ki amincewa da hakan ba. Abu mafi muhimmanci a gare mu a yanzu shi ne Allah ya bamu zaman lafiya,” inji shi.