Monday, September 25, 2023
GidaSiyasaGwamnatin Amurka ta taya zaɓaɓɓen shugaban Najeriya murna

Gwamnatin Amurka ta taya zaɓaɓɓen shugaban Najeriya murna

Kasar Amurka na taya zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da daukacin shugabannin siyasa da ‘yan Najeriya murnar gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya cikin nasara.

A cikin wata sanarwa da Amurka ta fitar ta ce zaben da aka gudanar na nuna sabon zamani ga siyasar Najeriya da dimokuradiyyar da ke nuna bambancin ra’ayi da ya shafi yakin neman zabe da kuma buri na masu kada kuri’a a Najeriya.

Don haka gwamnatin ta bi sahun sauran masu sa ido na kasa da kasa wajen yin kira ga INEC da ta inganta a yankunan da suka fi bukatar kulawa gabanin zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.

Harwayau sanarwar iamar yadda kafar NTA News24 ta ruwaito ta yaba da yadda kungiyoyin fararen hula da kafafen yada labarai ke taka rawar gani wajen inganta ka’idojin zabe da kuma tattaunawar siyasa kan batutuwa masu mahimmanci ga ‘yan kasa.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments