Ƴan bindiga sun kashe sojoji a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce ƴan bindiga sun kashe sojoji biyar a ƙauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe.

Ƙauyen na Wanzamai wanda ke kan iyakar jihar Zamfara da Katsina, na fuskantar matsin lamba daga maharan.

Wasu mazauna yankin sun shidawa BBC cewa sojojin sun yi ƙoƙarin kai ɗauki ne a garin na Wanzamai bayan jin ƙarar harbe-harbe.

A cewar wani matafiyi da ya shaidi lamarin “da misalin karfe biyu zuwa uku na dawo daga Abuja bayan na wuce Yankara da ke kan iyakar Katsina da Zamfara, muka tarar jami’an tsaro sun rufe hanya. Daga baya sai muka fahimci cewa mahara ne suka bude wa wata motar sojoji wuta kuma suka kashe duka sojoji biyar da ke ciki.”

” Kuma ganin cewa babu sadarwa yankin muna sa ran sojojin na sintiri ne maharan suka far musu suka bude musu wuta suka kuma kwashe musu makamai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa su suka taimaka wa yan sandan da suka kwashe gawawwakin sojojin.

Sama da wata daya Kenan da katse sadarwa a wasu yankunan jihohin Zamfara da Katsina, tare da rufe kasuwannin mako-mako a wani bangare na tsaurara matakan yaki da ƴan bindiga.