Ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari jihar Filato

Rahotanni daga Filato sun ce an kai wani hari da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 10 tare da ƙone gidaje a wani hari da ƴan bindiga da ba a tantance ba suka kai a Te’egbe a ƙaramar hukumar Bassa.

Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Mr Dan Manjang, wanda ya tabbatar wa majiyar mu ta BBC faruwan lamarin ya ce zuwa yanzu ba a tantance adadin hasarar rayuka da dukiya ba.

Wasu rahotanni sun ce an kai harin ne a cikin dare zuwa wayewar safiyar Juma’a inda ƴan bindigar suka buɗe wuta tare cinna wa gidaje wuta.