Saturday, January 16, 2021
Gida Blog

Hotunan auren tsohon Kakakin majalisar wakilai da ƴar Gwamnan jihar Kebbi

An fara shagulgulan bikin auren Barista Aisha Sa'idu Shinkafi, ƴar Gwamnan jihar Kebbi da ta tashi a gabansa da angonta, tsohon Kakakin majalisar wakilan tarayya Dimeji Bankole, ɗan jihar Ogun. Za a ɗaura auren su a yau Asabar da izinin Allah.

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya sarawa mazan jiya

Mai girma Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya bi sahun miliyoyin ƴan Najeriya wurin tunawa tare da jinjina ga mazan jiya a yayin bikin tunawa da su na shekarar 2021 da aka gudanar a yau Juma'a, wato dakarun Sojoji da suka sadaukar da rayukansu domin kare ƙasa. Kanal Sama'ila Yombe Dabai...

Ƙanin Kwankwaso ya zama sabon Hakimin Madobi

Majalisar masarautar Ƙaraye ta jihar Kano ta amince da naɗin Sale Musa Kwankwaso (Baba) a matsayin sabon Hakimin Madobi, kuma Makaman Ƙaraye. Naɗin nasa ya biyo bayan rasuwan mahaifinsa Alhaji Musa Saleh Kwankwaso (Majidaɗin Kano) wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Disamban 2020. Kafin naɗin Sabon Hakimin Madobi...

DA ƊUMI-ƊUMI: Sarkin Kauru, Jaafaru Abubakar ya rasu

Rahotanni dake fitowa daga jihar Kaduna na bayyana rasuwan Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Jafaru Abubakar CFR. Sarkin ya rasu a wannan yammaci yau Alhamis kamar yadda masarautar ta fitar da sanarwa.

DA ƊUMI-ƊUMI: Ma’aikatar Ilimi ta sake sanar da ranar buɗe makarantu

Ma'aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da matsayarta game da sake buɗe makarantu bayan yin duba kan lamarin kamar yadda ta bayyana a ranar 12 ga wannan wata. Sanarwar da ta fito da sa hannun Daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar Ben Bem Goong ta ce har yanzu ranar komawa makaranta shine 18 ga watan...

An yi garkuwa da ƴan kasuwar Kano mutum 27

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ƴan kasuwa ashirin da bakwai na Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano a kan hanyarsu ta zuwa garin Aba da ke jihar Abia. Majiyarmu ta Jaridar Daily Nigerian ta intanet, ta ruwaito ƴan kasuwar na kan hanyarsu ta zuwa Aba saro kayan...

Gwamna Zulum ya biya kuɗin dashen Ƙodar wani matashi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Talata ya amince da sakin naira miiyan goma (N10m) don ceton rayuwar Mbahi Sarki Suleiman, mai shekaru 29 ɗalibi a jami’ar Maiduguri, wanda ke matukar aikin dashen ƙoda. Dalibin ɗan asalin garin Yara ne dake ƙaramar hukumar Hawul da ke kudancin...

DA ƊUMI-ƊUMI: A karo na biyu majalisar dokokin Amurka ta sake tsige Trump

Majalisar wakilan tarayyar Amurka ta tsige shugaban ƙasar mai barin gado Donald Trump. Wannan shine karo na biyu da majalisar ke tsige shugaba Trump duk da cewa bata samu goyon bayan majalisar dattawar kasar ba, wadda ita ce za ta zartar da abin da ƙaramar majalisar ta yanke da goyon bayanta ga ƙudirin tsige...

IFTILA’I: Tankunan Mai biyu na wani ɗan kasuwa sun ƙone a mako ɗaya a jihar Kebbi

A ranar Lahadin makon jiya Allah ya ƙaddari ƙonewar wata tankar mai na wani ɗan kasuwa a garin Saminaka ta jihar Kebbi, Alhaji Abdul-Hamid Musa Saminaka, wanda a wannan iftila'in direban direba motar ya mutu. Iftila'in makon jiya. Wakilin Hausa Daily Times ya wuce ta garin...

DA ƊUMI-ƊUMI: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar 2020

Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa, NECO, ta fitar da sakamakon jarabawar kammala babbar sakandare ta shekarar 2020 wato SSCE. Shugaban hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne ya sanar da fitar da jarabawar yayin ganawa da manema labarai a Hedikwatar ta da ke Minna, fadar jihar Neja.A cewarsa, sakamakon jarabawar na wannan...

Biyo mu

0FansLike
0FollowersFollow
217FollowersFollow
0SubscribersSubscribe